Za mu yi bincike a kan kadarorin da gwamnatoci suka ƙwato tun daga 1999 - Majalisar wakilan Najeriya
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Majalisar wakilan Nijeriya za ta gudanar da bincike a kan dukkan kadarorin da gwamnatocin da suka gabata suka kwace tun bayan dawowar mulkin demokuraɗiyya a shekarar 1999.
Kafar yada labarai ta Daily trust ta ruwaito cewa, hakan ya biyo bayan nuna damuwa da Majalisar ta yi kan abin da ta kira rashin gaskiya da kuma gazawar adana bayanan kadarorin.



