EFCC ta fara bincike a kan mutane biyu da ta kama a filin jirgin saman Malam Aminu Kano kan zargin ɓoye Dala $461,600

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasa EFCC, reshen Kano ta fara binciken wasu mutane biyu, Jamilu Shuaibu Waya da Usman Namadi, bisa zargin boye dala $461,600 da ba su bayyana wa jami’an Kwastam ba a Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
An kama mutanen ne bayan sun dawo daga Dubai ta jirgin Ethiopian Airline ET941, inda suka bayyana wasu kudade amma binciken jami’an Kwastam ya gano karin kudaden dala da ba a bayyana ba.
Hukumar Kwastam ta ce wannan ya saba wa dokar hana safarar kudade ba bisa ka’ida ba, sannan ta mika mutanen tare da kudaden ga EFCC domin ci gaba da bincike da yiwuwar gurfanar da su a kotu.
Shugabannin EFCC da Kwastam a Kano sun yaba da hadin gwiwar hukumomin biyu wajen yaki da safarar kudade da sauran laifukan hada-hadar kuɗi a Najeriya.
