Koma Labarai
Shari'a

Kotun ta tsare wani ɗan Hisbah a gidan yari bisa zarginsa da cin amanar wata mata a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotun ta tsare wani ɗan Hisbah a gidan yari bisa zarginsa da cin amanar wata mata a Kano

Kotun Majistret mai lamba 11 da ke zaman ta a Gyaɗi-gyaɗi ƙarkashin mai Shari'a Rabi Abdulƙadir, ta aikewa da wani ɗan Hisbah gidan gyaran hali bisa zarginsa da cin amanar wata mata, baya da ta bashi kuɗi domin ya gina mata rijiyar Burtsatse amma ya gaza cika alƙawari.

Tunda farko mai ƙara Fatima Abubakar Sharada, ta garzaya ofishin ’yan sanda inda ta kai ƙarar Sulaiman Abba Isa Sharada Ja’en, bisa zargin ta ba shi kuɗi domin a gina mata rijiyar burtsatse don yin sadakatul jariya, amma hakan bai samu ba.

Bayan kammala binciken ’yan sanda, aka tura su Kotun Majistare mai lamba 11 da ke zamanta a Gyadi-Gyadi, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Rabi Abdulkadir, bisa tuhumar zamba cikin aminci da kuma cin amana.

Bayan karanta masa tuhume-tuhumen, ya musanta. Mai gabatar da ƙara ta buƙaci a ba su wata rana domin su kawo shaidunsu a kotu, inda kotun ta amince tare da sanya ranar 2/9/2026, sannan ta aika da shi gidan gyaran hali.

Mai Shari’a ta waiwayi mai ƙara, inda ta ce yar uwarta ce mijinta ya rasu, kuma tana son a gina masa rijiyar burtsatse. Ta ce ta nemi wanda ake ƙara, a matsayinsa na ɗan Hisba, ta ba shi Naira dubu ɗari biyar da hamsin, inda ya ce za a gina rijiyar a garin Dutsen Karya. Amma daga bisani ba a gina rijiyar ba, har ma ta ce ya kawo mata takardar godiya daga hukumar Hisba.

Kotun ta waiwayi wanda ake ƙara, amma ya ce tabbas ya gina rijiyar a Tukuntawa, saboda an samu matsalar wuri a inda aka fara magana. Ya kuma ce tun farko ba ita ce ta ba shi kuɗin ba, kuma sun yi shawara da ita cewa, a matsayinsa na ɗan Hisba, shi ne ya kamata ya nemo inda za a gina rijiyar.

Ready to PlayDala FM88.5 FM