Zan kawo ƙarshen matsalar tsaro cikin shekara ɗaya idan aka zaɓe ni a shugabancin Nijeriya - Atiku Abubakar
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni sun bayyana cewa, Ɗan takarar shugaban Nijeriya na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce zai kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya cikin shekara guda da hawansa mulki, muddin ya lashe zaɓe shekarar 2027.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a yayin wata hirar sa da BBC Hausa.
Tun bayan kaɗa gangar siyasa gabanin zaɓen shekarar 2027, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ci gaba da jan hankalin jama’a, musamman sakamakon wasu manufofin da ya bayyana, ciki har da alkawarinsa na baya-bayan nan na dawo da tallafin man fetur.
Waɗannan kalamai na Atiku Abubakar dai sun jawo martani daga gwamnati da kuma ƴan Nijeriya, da dama.



