Matsanancin rashin ruwa ya kusa zama tarihi a Kano - Kwamishina

Kwamishinan Ruwa da Muhalli da Sauyin Yanayi na Jihar Kano, Dakta Ɗahir Muhammad Hashim, ya tabbatar da cewa matsanancin ƙarancin ruwa ya kusa zama tarihi a jihar.
Dr. Ɗahir ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar bayan ya kai ziyarar gani-da-ido zuwa ma’ajiyar ruwa ta Goron Dutse a ranar Litinin 14 ga watan Satumba, 2026.
A cewar sa, "A ziyarar da na kai na ga cewa an kammala aikin gyara tare da wankewa da liƙe dukka fayif-fayif ɗin da ke cibiyar rarraba ruwan sha ta jihar mai tsawon kilomita 15.6," in ji shi.
Hashim ya ƙara da cewa, an yashe tare bushe dukka matattarar ruwan guda uku da su ke tara ruwa har lita miliyan 40.4, inda ya ƙara da cewa su ma tsoffin fayif-fayif ɗin an musanya su da na zallar ƙarfe da za su kasance mahadi-ka-ture.
“A halin yanzu ana ta aiki Ja'in da na’in Kuma daki-daki. Da yardar Allah, zuwa ƙarshen watan nan za mu fara gwajin sakin ruwan," in ji shi.
“Ina mai tabbatar wa al'ummar Kano cewa zamanin kamfar ruwan sha ya kusa zuwa ƙarshe. Wannan sabon salon aikin samar da ruwa ya samu ne sakamakon hikima da hangen nesa ta Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf,” in ji Hashim



