Koma Labarai
Labarai

An gudanar da jana'izar hadimin Gwamnan Kano da ya rasu a hatsarin tirela.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An gudanar da jana'izar hadimin Gwamnan Kano da ya rasu a hatsarin tirela.

An gudanar da jana'izar Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf kan ƙungiyoyi, Alhaji Sani Muhammad Hotoro, wanda aka fi sani da Dan Sani, bayan ya rasu a wani hatsarin tirela.

Rahotanni sun bayyana cewa hatsarin ya faru ne ranar Alhamis a kan titin Hotoro Eastern Bypass, kusa da gidan man Gade-Gade.

Majiyar labarin ta ce Ɗan Sani ya rasu tare da ɗaya daga cikin ma’aikatansa, inda shaidu suka bayyana cewa ya rasu ne a wurin da hatsarin ya afku.

An binne gawar Marigayin ne a Maƙabartar Tarauni da ke Kano, a ranar Juma'a 11 ga watan Satumba, 2026.

Ready to PlayDala FM88.5 FM