An ƙwace asusun Whatsapp, ɗin shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin jihar Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Rahotanni sun bayyana cewa masu kutse sun ƙwace asusun WhatsApp, na shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokokin Jihar Kano, kuma ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dala Hon. Lawan Hussaini Cheɗiyar Yan Gurasa.
Wannan na cikin sanarwar da Mai Taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Malam Nasa’i Abdullahi, ya fitar ga manema labarai.
Sanarwar ta kuma buƙaci jama’a da su yi taka-tsantsan tare da yin watsi da duk wani saƙo da aka tura musu daga asusun WhatsApp ɗin na Hon. Usaini Dala, har sai an dawo da ikon amfani da shi.
Haka kuma, Sanarwar ta ƙara da cewa, za a sanar da jama’a da zarar an warware matsalar tare da dawo da asusun, kamar yadda kafar Arewa Updates ta ruwaito.



