Koma Labarai
Shari'a

Kotu za ta yanke hukunci kan shari'ar tatsar bayanan wayar NSA Nuhu Ribaɗo da ake yi wa El-Rufa'i

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu za ta yanke hukunci kan shari'ar tatsar bayanan wayar NSA Nuhu Ribaɗo da ake yi wa El-Rufa'i

Babban kotun tarayya da ke Abuja ta sanya ranar 26 ga Oktoba domin yanke hukunci kan ƙarar neman a wanke tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, daga tuhumar da ake masa, sakamakon zargin sa da hannu wajen tatsar bayanai a wayar tarho da hukumar tsaro ta DSS ta shigar.

Ana tuhumar El-Rufai ne da laifukan da suka shafi karya dokokin tsaron ƙasa, da zargin ya taɓa sauraron tattaunawar wayar tarho ta Nuhu Ribadu, mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro NSA.

El-Rufai ya gabatar da ƙarar neman a yi watsi da tuhumar da ake masa, ya ce hujjojin da aka gabatar ba su isa a ci gaba da shari’ar ba, kamar yadda Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ready to PlayDala FM88.5 FM