Koma Labarai
Tsaro

Amnesty ta buƙaci a gudanar da bincike a kan harin soji da ya kashe fararen hula 100 a Zamfara

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Amnesty ta buƙaci a gudanar da bincike a kan harin soji da ya kashe fararen hula 100 a Zamfara

Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty International, ta buƙaci hukumomin su gudanar da bincike kan harin jirgin saman soji da ya kashe aƙalla fararen hula 100 a kasuwar Tumfa da ke Karamar Hukumar Zurmi a Jihar Zamfara.

Hakan na cikin sanarwar da ƙungiyar Amnesty International ta wallafa a shafin ta na Facebook.

Sanarwar ta ce da misalin ƙarfe 12 na rana jama’a a kasuwar mako mako sun ga jiragen soji suna shawagi a sama, sannan da misalin karfe 2 na rana jiragen suka dawo suka kai harin kan jama’a.

Kazalika sanarwar ta ce, mutane da dama da suka jikkata na karbar magani a Babban Asibitin Zurmi da na Shinkafi, yayin da shaidu suka bayyana cewa mata da yara na daga cikin wadanda suka fi mutuwa.

Kungiyar ta ƙara da cewa irin wannan lamari ya faru a watan Afrilu a Jilli da ke kan iyakar Jihohin Borno da Yobe inda aka kashe fararen hula sama da 100 a harin jirgin sama, kamar yadda kafar Arewa updates ta ruwaito.

Amnesty International ta ce ya zama wajibi a gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da gaskiya da daukar matakin doka kan duk wanda aka samu da laifi, tare da jaddada cewa dole ne a kare rayukan fararen hula a yayin gudanar da ayyukan tsaro.

Ready to PlayDala FM88.5 FM