Gwamnatin Kano duk wanda ya kawo rai ni a sha'anin jihar to a nuna masa ƙarfin mulki - Sarkin Kano

Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi na biyu, yayi kira ga Gwamnan Kano da cewa duk wanda ya kawo rai ni a sha'anin jihar to a nuna masa ƙarfin mulki domin babu ɗaga ƙafa ga duk wanda ya kawo rai ni.
Sarkin ya bayyana hakan ne a safiyar ranar Juma'a 29 ga Mayu, 2026, yayin ziyarar da ya kai wa gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnatin jihar Kano.
Khalifa Muhammadu Sanusi, ya ce ya kai ziyarar ne domin raya sunnar magabata zuwa fadar gwamnatin jihar, domin yi wa juna barka da Sallah, da kuma sada zumunci da yin Addu'ar Allah SWA ya maimaita mana cikin kwanciyar hankali da yalwal arziƙi.
Ya kuma bayyana cewa yanzu lokaci ne na tattauna muhimman batutuwa, domin kasancewar su ƴan gida ɗaya, inda ya yaba masa a kan abubuwan ya aikata na daidai, ciki har da ɓangaran ilimi, lafiya, gyare gyaran hanyoyi, da taimaka wa al'umma musamman na karkara.
A karshe sarkin ya kuma buƙaci gwamnatin Kano da ta saurari yankasuwa a kan abubuwan da suke nema na tallafi, kama daga gwamnatin Kano, har zuwa gwamnatin tarayya.
Wakilinmu na Masarautar Kano Shu'aibu Uba Minshawi ya rawaito cewa, sarkin ya kuma yi fatan gwamnatin tarayya za ta shigo jihar Kano, domin gabatar da muhimman ayyukan ci gaba masu yawa ga al'ummar jihar.



