Gwamnan Kano ya amince da karin albashi ga ma'aikatan jami'o'in jihar guda biyu
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da ƙarin albashi ga malamai da sauran ma'aikatan jami'o'in jihar guda biyu.
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwaman, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin 10 ga Agustan 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin albashin ya shafi jami'ar Aliko Ɗangote ta Wudil, da kuma Northwest da ke jihar Kano.
Kafar yaɗa labarai ta DCL Hausa ta ruwaito cewa, Sanarwar ta kuma ce za a fara aiwatar da biyan ne a watan Satumban 2026 mai kamawa.



