Jihar Kano na ci gaba da zama lafiya da kwanciyar hankali - Kwamishinan Ƴan Sanda

Rundunar ƴan sandan Kano, ta ce jihar na ci gaba da zama cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, duk kuwa da matsalar tsaron da aka fuskanta a kwanakin bayan nan.
Tashar Dala FM ta ruwaito cewa, Kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ne ya bayyana hakan a yayin taron manema labaran da ya gudanar a hedikwatar rundunar da ke unguwar Bompai a ranar Laraba 20 ga Mayu, 2026.
A cewar sa, "Hakan na zuwa ne biyo bayan dabaru da ake ɗauka domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron al'umma, biyo bayan umarnin da Babban Sufeton Ƴan Sanda na ƙasa ya bayar na aiki tukuru, da kuma gudanar da aiki tare da al'umma," in ji CP Bakori.
Sai dai ya ce duk da haka sun samu rahotanni na faɗace-faɗacen daba a birnin Kano, musamman unguwannin Fagge, titin IBB, da Hotoro, a cikin wannan lokaci.
Ibrahim Adamu Bakori, ya kuma ce a ƴan kwanakin bayan nan an samu matsalar tsaro a iyakokin Kano, da Katsina, da Kaduna.
Sai dai ce domin maganin waɗannan matsalolin jami'an Ƴan Sanda, tare da sauran hukumomin tsaro, a ƙarƙashin Join Task Force, sun canza dabarun aiki ta hanyar ƙara tura ma'aikata, da tattara bayanan sirri, da kuma ƙara sintirin Ƴan Sanda, da kuma kai hare-hare kan ƴan ta'adda.
A cewar sa matakan da aka dauka sun taimaka wajen kawo zaman lafiya a faɗin jihar Kano.



