Koma Labarai
Tsaro

Ƴan Sanda sun cafke mutumin da ake zargi da garkuwa da mutane tare da ƙwato bindiga AK-47 a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ƴan Sanda sun cafke mutumin da ake zargi da garkuwa da mutane tare da ƙwato bindiga AK-47 a Kano.

Rundunar ’Yan Sandan jihar Kano ta kama wani mutum mai suna Ibrahim Rabi'u, wanda ake zargi da hannu wajen garkuwa da mutane, tare da kwato bindigar AK-47 da alburusai masu rai guda 18 a dajin Falgore.

Kakakin rundunar CSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya bayyana cewa, an kama wanda ake zargin ne a ranar 18 ga Oktoba, 2026, yayin wani samame da jami’an ’yan sanda na sashen Doguwa suka gudanar tare da haɗin gwiwar mafarautan sa-kai, waɗanda aka fi sani da ’Yan Bula.

Ana zargin Rabi'u da hannu wajen garkuwa da Alhaji Kabiru Aliyu, mai shekaru 45, mazaunin ƙauyen Falgore.

Rahotanni sun bayyana cewa, wanda aka yi garkuwa da shi ya gane wanda ake zargin a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda ke gadinsa lokacin da yake tsare.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM