Kotun tafi da gidanka ta ci tarar gidan man MRS tarar dubu 100, bisa laifin siyar da mai lokacin tsaftar muhalli a Kano.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Kotun tafi da gidan ka ƙarƙashin jagorancin Alƙali Shamsuddin Ado Abdullahi, ta ci tarar wani gidan mai da ke kusa da tsohuwar Jami’ar Bayero ₦100,000 bisa samunsa yana sayar da mai a lokacin tsaftar muhalli a jihar Kano.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan da ta tabbatar da cewa gidan man ya karya dokar tsaftar muhalli.


