Sarki Khalifa Muhammadu Sanusi II ya naɗa Hakimai huɗu a masarautar Kano

Mai martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu, ya naɗa sababbin Hakimai guda huɗu a fadar sa, da suka haɗar da Sarkin arewa Alhaji Ɗahiru Shehu Giɗaɗo, da Mayanan Kano Alhaji Sa'adu Matawalle.
Sarkin ya kuma naɗa Barwan Kano Alhaji Faisal Abubakar Buhari, da kuma Kachallan Kano Alhaji Muhammad Ɗan Iya Ibrahim da aka naɗa a matsayin Hakimin Garin Malam.
Sarkin na Kano, ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan naɗa hakiman a fadarsa da ke Ƙofar Kudu, a ranar Juma'a 12 ga Yuni, 2026.
Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya kuma yi kira ga sauran hakimai da su basu haɗin kan da ya dace domin su samu damar gudanar da ayyukansu yadda ya kamata a masarautar ta Kano.
A cewar sa, "Mun naɗa hakiman ne bisa cancanta da kuma irin gudunmuwar da suke bayarwa don cigaban al'umma, da kuma masarautar Kano da ma ƙasa baki ɗaya, in ji shi.”
A nasu jawaban daban-daban sabbin hakiman sun godewa masarautar Kano da ta basu wannan matsayi, suna mai cewa za su ɗora aiki daga inda magabatansu suka bar musu don cigaba da taimakawa al'umma.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, taron naɗin ya samu halartar wakilan sarakunan jihar nan da ma na sassan Najeriya.

