Koma Labarai
Labarai

Mazauna yankin Rafin Ɗannana, zuwa Rimin Auzinawa, sun buƙaci Gwamnatin Kano ta sa ido domin tabbatar da an kammala aikin titin yankin.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Mazauna yankin Rafin Ɗannana, zuwa Rimin Auzinawa, sun buƙaci Gwamnatin Kano ta sa ido domin tabbatar da an kammala aikin titin yankin.

Mazauna yankin Rafin Dannana, da ke kan hanyar Zeenoor zuwa Tudun Yola zuwa Rimin Auzinawa, sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta sa ido domin tabbatar ganin an kammala aikin titin da ake yi a yankin, suna zargin cewa yadda aikin ke gudana na haifar da barazana ga rayuka da dukiyoyin al’umma.

Mazauna yankin sun ce ya zama wajibi gwamnati ta bibiyi aikin tare da tabbatar da cewa ɗan kwangilar yana gudanar da shi bisa ƙa’ida da kuma matakan da za su kare lafiyar jama’a sakamakon yadda aka tsaya da aikin.

Shugaban matasan yankin, Kwamared Al’amin Muhammad, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da matasan suka gudanar a unguwar, yana mai cewa ko da yake ma aikin da akai na farkon ma ba shi da inganci balle ayi batun na yanzu.

Ready to PlayDala FM88.5 FM