Kotu ta aike da Amarya gidan gyaran hali bisa zargin ta da kashe uwar gida ta hanyar daddatsa ta da Adda a Kano

Kotun Majistire mai lamba 2 da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Auwal Yusuf Sulaiman, ta aike da wata mata mai suna Safiya Hussaini, gidan gyaran hali bayan gurfanar da ita kan zargin kisan kai.
’Yan sanda ne suka gurfanar da Safiya Hussaini, mai kimanin shekaru 20, wadda ke zaune a ƙauyen Loko da ke Ƙaramar Hukumar Takai ta Jihar Kano.
Takardun tuhumar sun bayyana cewa, an zargin Safiya da samun saɓani da abokiyar zamanta, inda ta yi amfani da Adda ta sare ta, lamarin da ya yi sanadin rasuwarta.
A yayin zaman kotun, mai gabatar da ƙara ya bayyana cewa kotun ba ta da hurumin sauraron shari’ar, saboda haka ya roƙi a ba shi lokaci domin kammala bincike tare da gurfanar da ita a kotun da ta dace.
Mai Shari’a ya ɗage shari’ar na tsawon makonni biyu, sannan ya umarci lauyoyin gwamnati su duba kundin bincike domin ɗaukar matakin da ya dace.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma’il ya ruwaito cewa ana tuhumar Safiya Hussaini ne ƙarƙashin sashe na 221 na Penal Code.



