Rundunar Anti-Phone Snaching force ta kama wani ɗan shekaru 55 ɗauke da Sholisho sama da 100, a Kano.

Rundunar tsaro ta Anti illicit drugs and Phone Snaching force ta jihar Kano, ta kama Ali Sulaiman mai shekara 55, bisa samun sa da Sholisho sama da guda ɗari, da ake zargin yana sayar wa a yankin Audu Baƙo.
Kwamandan rundunar tsaron a Kano Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan ga Dala FM Kano, a ranar Litinin 7 ga watan Oktoba, 2026.
A cewar sa, "Bayan da muka samu bayanan sirri ne kan yadda mutumin yake sayar da kayan maye, muka tura jami'an inda suka kamo shi a ranar Lahadi, a yankin Audu Baƙo da ke Kano," in ji Nura.
Ya kuma ce akwai abin ban takaici kan yadda aka samu tsohon da laifin sayar da Sholisho, mai-makon a same shi da yin abinda ya kamace shi, musamman ma da shekaru suka ja.
Mutumin da ake zargin mai suna Ali Sulaiman mazaunin yankin Tarauni, ya ce ya kai kusan shekaru ashirin yana sha da kuma sayar da Sholisho a yankin Audu Baƙo.
A cewar sa, "Ina sayarwa da matasa masu jagaliyancin siyasa sholishon, kuma nima ina jagaliyancin a baya amma dai yanzu na daina iya sholishon nake sayarwa" in ji shi.
Ali Sulaiman ya kuma bayyana nadamar sa, inda ya ce har fasa auren sa aka yi saboda yana sha da sayar da Sholisho a Kano.
Daga bisani, Kwamandan rundunar tsaron ta Anti-Phone Snaching force a Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ya ce da zarar sun kammala bincike a kan tsohon za su miƙa shi inda ya dace domin ɗaukar mataki na gaba.
Nura sharaɗa, ya kuma gargaɗi dukkan masu sha da sayar da kayan maye a Kano, da su daina, domin duk wanda suka kamata da aikata laifuka ba za su saurara masa ba.



