Gwamnan Bauchi Bala Mohammed ya fice daga PDP ya koma APM
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, (Ƙauran Bauchi) ya sanar da ficewarsa daga cikin jam'iyyar PDP zuwa APM, bayan makwanni ana rade-radin makomarsa ta siyasa.
Gwamnan ya bayyana sauya shekar ne a ranar Asabar 2 ga watan Mayu, 2026, a gidan gwamnati da ke jihar Bauchi.
Ya kuma ce rikice-rikicen cikin gida da ke addabar PDP ne suka tilasta masa neman wata sabuwar jam’iyya domin tabbatar da makomar magoya bayansa gabanin zaben 2027.



