Koma Labarai
Labarai

An ƙaddamar da ƙungiyar ƴan jarida masu kawo rahoto kan sauyin yanayi a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
An ƙaddamar da ƙungiyar ƴan jarida masu kawo rahoto kan sauyin yanayi a Kano

An ƙaddamar da ƙungiyar ƴan jarida ta Kano Climate Change Journalists’ Network (KCCJN), ƙungiya irin ta ta farko ta 'yan jarida kan sauyin yanayi a Jihar Kano, domin samar da rahotanni masu inganci kan sauyin yanayi da ƙara wayar da kan al'umma kan batutuwan muhalli.

Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da cibiyar, Daraktan sauyin yanayi na Jihar Kano, Dr. Umar Sale Anka, ya ce wannan mataki ya zo a kan lokaci, yana mai cewa zai taimaka wa gwamnatin jihar wajen yaƙi da illolin sauyin yanayi ta hanyar wayar da kan jama'a da inganta tattaunawa game da manufofi.

Kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa, Ita ma mai ba da shawara ga gamayya, Dr. Hadiza Shettima, ta buƙaci 'yan jaridar da su mayar da hankali a kan alaƙar sauyin yanayi da wadatar abinci.

Dr. Hadiza ta kuma ce Afirka na daga cikin yankunan da sauyin yanayi ya fi shafa, musamman a fannin noma.

Sanarwar ta ce, an zaɓi Lukman Abdulmalik a matsayin shugaba, kuma babban edita na ƙungiyar, yayin da Zulaiha Danjuma ta zama edita, Hannatu Suleiman Abba manajan shirye-shirye, Abdulwahab Said Ahmad jami'in yaɗa labarai, da Muhammad Dahiru Lawal, mataimaki a fannin bincike, da Khadija Yahaya sakatare.

Sauran mambobin sun haɗa da Salisu Hamisu Ali, Dalal Salisu Musa, Jamila Adam Seyoji da Aisha Shehu Kabara.

An bayyana cewa ƙungiyar za ta ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin 'yan jarida, masu tsara manufofi, da masu bincike da abokan hulɗar ci gaba domin inganta sahihan rahotanni kan sauyin yanayi da dorewar muhalli a Kano.

Haka kuma, an kafa ƙungiyar ne sakamakon shirin HumanAngle SCOJA Fellowship, da aka gudanar tsakanin Nuwamban 2025 zuwa Afrilun 2026, domin inganta rahotannin sauyin yanayi a Najeriya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM