Koma Labarai
Labarai

Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi, ya naɗa sabon Sarkin Gumel

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnan jihar Jigawa Umar Namadi, ya naɗa sabon Sarkin Gumel

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da naɗin Dr. Lawan Ahmed Muhammad Sani, a matsayin Sarkin Gumel na 17, kwanaki uku bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi Sarkin Gumel Dr. Ahmed Muhammad Sani.

Sakataren Gwamnatin Jihar, Bala Ibrahim, ne ya sanar da naɗin a ranar Lahadi a Dutse, yana mai cewa kafin naɗin nasa an gudanar da shawarwari da majalisar masarautar Gumel da masu zaɓen sarki, bisa dokar masarautun jihar.

Dr. Lawan ya taɓa riƙe sarautar Ciroman Gumel a lokacin mulkin mahaifinsa, abin da gwamnatin jihar ta ce ya ba shi ƙwarewa da fahimtar al’adu da buƙatun masarautar Gumel.

Kafar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa, Gwamna Namadi ya yi kira ga al’ummar Gumel da su ba sabon sarkin cikakken goyon baya domin tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban masarautar.

Kazalika, Gwamnatin ta ce za a gabatar wa da sabon sarkin sandarmuƙa, (Sandar girma) a wani biki na musamman da za a gudanar nan gaba kaɗan.

Ready to PlayDala FM88.5 FM