Koma Labarai
Tsaro

Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta cafke magidanci ɗan Katsina kan zargin sayar da ƙwayoyi a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Rundunar Anti-Phone Snatching Force ta cafke magidanci ɗan Katsina kan zargin sayar da ƙwayoyi a Kano

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile ta'ammali da kayan maye, ta Anti Illicit Drugs and Phone Snatching Force a Kano, ta kama Janaidu Ɗanjuma Badamasi, mai shekaru 40, bisa zarginsa da sayar da ƙwaya Exol, da ake yi wa laƙabi da sha fara ka ga aljan, a ƙasan Gadar Kofar Nassarawa.

Kwamandan rundunar tsaron Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana wa Dala FM Kano, kama Magidancin a Kano.

Ya ce sun kama shi ne bayan da suka samu bayanan sirri kan yadda ake hada-hada wajen sayar da kayan maye a ƙasan Gadar ta Kofar Nassarawa.

A cewar sa, "Bayan da muka samu bayanan sirrin ne muka tura jami'an mu na Operation Damisa Ƙi Sabo, inda suka kai sumame ƙasan gadar tare da kamo Magidancin ɗauke da tarin ƙwayoyin da ake zargin yana sayarwa," in ji Nura.

Ya ce sun lura da cewa mafi yawan aikata laifuka ana aikata su ne sakamakon shan miyagun ƙwayoyi, a don haka suka bi umarnin Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, wajen ƙara matsa lamba kan yaƙi da tam'ammali da ƙwayoyin da sauran kayan maye a jihar.

Da yake bayyana nadamar sa, magidancin da aka kama, Janaidu Ɗanjuma Badamasi, ɗan asalin yankin Jibiya da ke jihar Katsina, ya ce tsayawar sana'ar da yake yi ta Dako ce ta sanya shi fara sayar da ƙwayoyin, amma dai daga wannan ba zai ƙara ba.

Daga bisani Kwamandan rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ya ce za su miƙa magidancin gurin da ya dace domin ɗaukar mataki na gaba a kan sa.

Ya kuma gargaɗi masu sha da dillancin kayan maye da su daina yana ma cewa duk wanda ya shigo komar su ba za su saurara masa ba.

Nura Sharaɗa ya kuma buƙaci iyaye da su ƙara sanya idanu a kan shige da ficen ƴaƴansu, tare da sanin irin abokan da suke yi, domin gujewa lalacewar tarbiyyar su.

Ready to PlayDala FM88.5 FM