Jargin farko ɗauke da Alhazai 560 ya sauka a Najeriya
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Hukumar kula da aikin Hajji ta ƙasa NAHCON, ta bayyana cewa jirgin farko na MaxAir, ɗauke da Alhazan jihar Nassarawa 560, ya sauka a birnin Tarayya Abuja daga Jeddah, bayan kammala aikin hajjin 2026.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Hukumar ta NAHCON, ta bayyana hakan ne ranar Laraba 3 ga Yuni, 2026, a shafin ta na Facebook.
Hukumar ta kuma ce Alhazan na jihar Nassarawa sun sauka da misalin ƙarfe 09:27 na daren ranar Talata 02 ga watan Yuni, 2026.
Aƙalla dai sama daga Alhazai 1.7 ne suka gudanar da aikin hajjin 2026, a ƙasar Saudiyya, da suka halarta daga ƙasashe daban-daban na duniya.



