Koma Labarai
Labarai

NNPC ya rage Naira 66 kan kowace litar man fetur a Nijeriya.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
NNPC ya rage Naira 66 kan kowace litar man fetur a Nijeriya.

Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL, ya ƙaddamar da rangwamen Naira 66 kan man fetur ga kwastomominsa a faɗin Nijeriya da ke amfani da manhajar NNPC Fuel App.

Kamfanin ya bayyana cewa shirin rangwamen, wanda ya fara ranar 1 ga Oktoba, zai ci gaba har zuwa 7 ga watan na shekarar 2026.

A cewar Kamfanin, ana gudanar da tsarin ne a gidajen mai na NNPC da ke sassa daban-daban na ƙasar kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da al'umma ke ta kiraye-kiraye ga gwamnatin tarayya da ta rage farashin la'akari da tsadar da ya yi, domin a gidajen man ƴan kasuwa ana sayar da litar man Naira 1,410, wasu dagajen sama da haka.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM