Koma Labarai
Shari'a

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta soke tikitin takarar Farfesa Isa Ali Pantami na Gombe a jam'iyyar PDP.

Hassan Mamuda Ya'u 16 views
Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta soke tikitin takarar Farfesa Isa Ali Pantami na Gombe a jam'iyyar PDP.

Babbar Kotun Tarayya da ke zaman ta a jihar Gombe, ta umarci jam’iyyar PDP ta sake gudanar da zaɓen fidda gwani na takarar gwamnan jihar Gombe.

Mai shari’a Amina Aliyu Mohammed ce ta yanke hukuncin a ranar Alhamis 24 ga watan Satumban 2026.

Hukuncin na zuwa ne biyo bayan sauraron ƙarar da Usman Aliyu Garry ya shigar yana ƙalubalantar fitowar Farfesa Isa Ali Pantami, a matsayin ɗan takarar jam’iyyar, kamar yadda Jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kazalika, kotun ta kuma bada umarnin a sake yin zaɓen fidda gwani.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM