Nan gaba kaɗan za'a gudanar da bikin sabuwar shekarar kalandar Shari'a a Kano - Baba Jibo
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Hukumar da ke kula da harkokin Shari'a ta jihar Kano, ta ce manyan kotunan ƙasar nan sun dawo bakin aiki bayan kammala hutu na tsahon watanni biyu da suka gabata.
Mai magana da yawun babbar Kotun jihar Kano, Baba jibo Ibrahim ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Talata 22 ga watan Satumba, 2026.
Baba Jibo ya bayyana cewar, alƙalan manyan kotunan su kan tafi huta ne domin ƙwaƙwalwarsu ta huta sakamakon aikace-aikacen da ya yi musu yawa.
Ya kuma bayyana cewar ana ware wasu alƙalan waɗanda basa tafiya hutu domin gudanar da shari'ar gaggawa.
Baba jibo ya kuma ƙara da cewa, kalandar sabuwar shekarar Shari'ar ta fara yanzu, kasancewar kalandar Shari'a ba daidai ta ke tafiya da kalandar gama gari ba.



