Koma Labarai
Labarai

Hukumar Shari'a ta fara rangadi zuwa ga malaman musulunci don lalubo hanyoyin gyaran tarbiyyar al'umma a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar Shari'a ta fara rangadi zuwa ga malaman musulunci don lalubo hanyoyin gyaran tarbiyyar al'umma a Kano.

Hukumar Shari'a ta jihar Kano ta fara rangadi zuwa ga malaman addinin musulunci da ke jihar, domin lalubo hanyoyin gyaran tarbiyyar matasa, da daƙile cin mutuncin da wasu ƴan siyasa suke wa junan su a shafukan sada zumunta.

Shugaban Hukumar Shari'a a jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya jagoranci hukumar domin kai ziyarar a ranar Talata 17 ga watan Nuwamba, 2026.

Hukumar ta fara da kai ziyarar ne gidan fitaccen malamin addinin musulunci Sheikh Abdulwahaf Abdullah, da ofishin Shugaban Majalisar Malamai na yankin Arewa, Sheikh Ibrahim Khalil, sai kuma Shugaban Ƙadiriyya na Afrika, Sheikh Ƙariballah Sheikh Nasiru Kabara.

Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ya ce ziyarar rangadin na da nufin lalubo hanyoyin gyaran tarbiyyar al'ummar jihar Kano, musamman matasa, da daƙile munanan kalaman da wasu ƴan siyasa ke jifan junan su da su a shafukan sada zumunta, da sauran matsalolin da ake fuskanta a jihar Kano.

Da yake nasa jawabin, Kwamishina na biyu a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, cewa ya yi akwai buƙatar malaman su ya kira ga limamai da malamai, da su faɗakar da al'umma don magance matsalolin da ake fuskanta a Kano.

Ya kuma ce hukumar shari'ar ta buƙaci malaman da su yi kira ga limamai da malamai da su ƙara ƙoƙari wajen faɗakar da al'umma kan illar bidiyon Raƙumin AI, da wasu ke yaɗawa a shafukan sada zumunta, wanda ke ɗura ashar, la'akari da yadda hakan ke lalata tarbiyyar yara.

Dukkanin malaman sun sha alwashin bada gudunmawar su ta bangarori daban-daban, domin ganin an magance matsalolin da ake fuskanta tare da gyaran tarbiyyar al'umma a jihar Kano.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM