Koma Labarai
Labarai

“Matashi ɗan jihar Kano ya yi fice a dandalin Facebook da TikTok”

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
“Matashi ɗan jihar Kano ya yi fice a dandalin Facebook da TikTok”

Wani matashi daga jihar Kano mai suna Saleem Top, ya samu karɓuwa sosai a kafafen sada zumunta musamman Facebook da TikTok, saboda irin contents ɗinsa masu ilmantarwa da faɗakarwa.

Saleem Top wanda ya shahara wajen ƙirƙirar Islamic contents, na ɗaya daga cikin matasan Arewa da suka yi fice a social media cikin shekarun baya-bayan nan.

Masu bibiyar harkokin digital media sun bayyana cewa, matashin ya samu ɗumbin mabiyan da ke bibiyar bidiyoyinsa saboda yadda yake gabatar da saƙonni cikin harshen Hausa mai sauƙi da fahimta.

A cewarsa, ya fara content creation, ne domin amfani da shafukan sada zumunta wajen yaɗa abubuwan da za su amfani matasa da al’umma baki ɗaya.

“Babban burina shi ne in amfani da kafafen sada zumunta wajen ilmantarwa da fadakarwa,” in ji Saleem Top.

Rahotanni sun nuna cewa Saleem Top na daga cikin waɗanda suka fi samun mabiya a Facebook a Arewa Najeriya, lamarin da ya ƙara sanya sunansa cikin fitattun influencers daga yankin Arewa.

Mabiyansa na yabawa da yadda yake haɗa nishaɗi, ilmantarwa, da nasiha cikin sauƙi da fahimta, musamman ga matasa masu amfani da TikTok, da Facebook.

Masana harkokin shafukan sada zumunta na ganin cewa, ci gaban da yake samu na nuna yadda matasan Arewa ke amfani da internet, wajen ƙirƙirar sana’o’i da kuma gina suna.

Waɗannan dalilai ne ya sa ma yake ci gaba da samun karɓuwa daga mutane da dama, ana kallon Saleem Top a matsayin ɗaya daga cikin sabbin fitattun creators daga Arewacin Najeriya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM