An zargi jami'an tsaron DSS da na gidan gyaran hali da hana mutane shiga sauraron shari'ar Omoyele Sowore.

An yi zargin cewa jami’an Hukumar tsaron farin kaya (DSS) tare da jami’an Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya, sun hana mutane shiga cikin harabar kotu domin sauraron shari’ar ɗan gwagwarmaya kuma mai wallafa labarai, Omoyele Sowore.
Rahotanni sun ce jami’an tsaron sun toshe hanyoyin shiga kotun tare da hana wasu masu sha’awar sauraron shari’ar, ciki har da magoya baya da masu rajin kare haƙƙin bil’adama, samun damar shiga kotun.
Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce kan batun buɗaɗɗiyar shari’a da kuma damar jama’a na halartar zaman kotu, musamman a shari’o’in da ke jan hankalin al’umma.
Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomin DSS da na Gidajen Gyaran Hali ba su fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da zargin ba.
A safiyar Larabar nan ne dai jami'an suka kai Sowore kotun bisa zarge-zargen da ake yi masa.
Omoyele Sowore, wanda ya shahara a matsayin mai rajin kare haƙƙin ɗan adam, kuma ɗan takarar shugaban ƙasa, na fuskantar shari’a kan wasu zarge-zarge da ake yi masa a kotu.



