Koma Labarai
Labarai

Karota ta kama direban motar da ake zargi da buge jami'in ta har ya samu karaya 6 a sassan jikin sa a Kano.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Karota ta kama direban motar da ake zargi da buge jami'in ta har ya samu karaya 6 a sassan jikin sa a Kano.

Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA) ta samu nasarar cafke wani direban mota da ake zargi da yin gudun hijira bayan ya buge wani jami’in hukumar a yayin da yake kokarin kaucewa binciken jami’an hukumar a Ɗanbatta.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharaɗa, ya fitar ga manema labarai.

Sanarwar ta ce, lamarin ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 3:00 na rana, lokacin da jami’an KAROTA ke gudanar da aikin bincike a yankin Ɗanbatta.

A cewar sanarwar, a yayin da jami’an ke ƙoƙarin tsayar da motar ne sai direban ya yi yunƙurin tserewa, inda ya buge Mataimakin Shugaban tawagar Sintiri a yankin, (2IC) Malam Nasir Abdullahi, da akafi sani da Baba Nasiru.

Bayan faruwar lamarin, Malam Nasir Abdullahi ya suma, tare da samun raunuka masu tsanani da suka haɗa da karyewar kasusuwa daban-daban na jikinsa.

Cikin wata sanarwar da Mataimaki na musamman ga Shugaban Hukumar KAROTA, Mu'azzam Mansur Kurawa, ya fitar a ranar Lahadi 23 ga Agustan 2026, ya ce jami'in hukumar ya samu karaya guda shida a sassa daban-daban na jikin sa.

Sai dai sanarwar da KAROTA, ta fitar, ta ce duk da cewa direban ya samu damar tserewa daga wurin da lamarin ya faru, jami’an leken asiri na hukumar sun ci gaba da bin sawunsa, har sai da suka yi nasarar gano inda yake tare da cafke shi.

Sanarwar ta kuma ce, daga bisani an miƙa wanda ake zargin ga sashen kula da zirga-zirgar ababen hawa na Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano da ke Kofar Nassarawa, domin ci gaba da gudanar da bincike da kuma daukar matakin da ya dace na shari’a.

A halin yanzu, Malam Nasir Abdullahi yana kwance a Sashen Kula da Marasa Lafiya Masu Tsananin Ciwo (ICU) na Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, inda binciken likitoci ya tabbatar da cewa ya samu karyewar kasusuwa guda shida sakamakon raunukan da ya ji a hatsarin.

Hukumar KAROTA na ci gaba da addu’ar samun saukin gaggawa ga jami’in nata, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da yin aiki tukuru wajen tabbatar da bin dokokin hanya da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Ready to PlayDala FM88.5 FM