Majalisar dokokin Kano ta dakatar da ɗan majalisar Nassarawa, Yusuf Bello Aliyu na tsawon watanni uku.
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Majalisar dokokin jihar Kano ta dakatar da ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Nassarawa, Yusuf Bello Aliyu na tsawon watanni uku.
A zaman majalisar na ranar Laraba 21 ga watan Oktoba, 2026, majalisar ta ce ɗan majalisar zai kauracewa shiga dukkanin al'amuran da suka shafi harkokin majalisar har zuwa wancan lokaci.
A kwanakin bayan nan ne dai majalisar ta bayyana gayyatar ɗan majalisar, biyo bayan ganin wani bidiyo da ɗan majalisar ya riƙe kunnuwan Zomo, yana faɗar wasu kalamai da aka danganta da cin mutuncin Gwamnan Kano.
Da yake karin haske bayan zaman majalisar, Lawan Husaini Dala, ya ce ya zama wajibi ga Yusuf Bello Aliyu, ya zo ya nemi afuwar a gaban majalisar.



