Koma Labarai
Shari'a

Shari'ar garkuwa da mutane: kotu ta fara sauraren shaidu a Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Shari'ar garkuwa da mutane: kotu ta fara sauraren shaidu a Kano

Babbar Kotun jiha Kano mai lamba 18 ƙarƙashin jagorancin mai shari'a Fatima Adamu, ta fara sauraren shaidu a ƙunshin tuhumar da gwamnatin Kano ta ke yi wa wani mutum mai suna Abdussalam Muhammad, wanda ake tuhuma da laifin garkuwa da yaro domin neman kuɗin fansa.

Ƙunshi zargin ya bayyana cewar wanda ake tuhuma ya haɗa baki da wasu waɗanda a yanzu sun tsere.

An bayyana cewar mutanen sun je Ƙofar gabas da ke ƙaramar hukumar Ƙiru, inda suka yi garkuwa da wani ƙaramin yaro a ranar 3 ga watan Mayu, 2025.

Wakilinmu Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, ƙunshin zargin ya bayyana yadda suka turo lambar asusun banki daga nan ne kuma aka bi diddiginsu aka kama Abdussalam Muhammad.

A zaman kotun na ranar Talata 7 ga watan Yuli, 2026, an saurari shaidun masu gabatar da ƙara, an kuma ɗaga zaman zuwa ranar 7 ga Oktoba, 2026.

Ready to PlayDala FM88.5 FM