NDC ta tsayar da Comrd. Aminu Gwarzo a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Jam’iyyar NDC ta tsayar tsohon mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a matsayin ɗan takarar gwamnan Kano.
Jagoran jam'iyyar NDC, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ne ya sanar da hakan a ranar Alhamis 28 ga Mayu, 2026.
Kazalika, jam'iyyar ta kuma tsayar da tsohon mataimakin Gwamnan Kano Dr. Nasiru Yusuf Gawuna, a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya.
Da yake jawabi mai kama da martani, fitaccen ɗan jaridar nan Ja'afar Ja'afar ya ce, “Ba ni da shakku a kan nagartar Cmrd, amma na so Gawuna ya samu ticket ɗin gwamna na NDC domin ya yi wa butulci fashin kwakwa. Ita APC kamar wuƙar pawa take: da ‘yar uwarta ake wasa ta”

