Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan Durbar da ayyukan hawan doki zuwa wani lokaci a birnin jihar

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano ta hana hawan Durbar da ayyukan hawan doki zuwa wani lokaci a birnin jihar

Gwamnatin Jihar Kano ta sanya takunkumi a kan duk wani nau’in jerin gwanon Durbar, da ayyukan hawan doki a cikin birnin jihar, har zuwa wani lokaci da ba ta bayyana ba.

Wannan na cikin sanarwar da babban Daraktan Gwamnatin jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Lahadi 27 ga watan Satumban 2026.

Sanarwar ta ce matakin ya biyo bayan wani taron gaggawa na Majalisar Tsaro ta Jihar da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Kano, inda aka duba yanayin tsaro da ke kewaye da shirye-shiryen gudanar da ayyuka hawan.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM