Kwalejin ASCON na ci gaba da horas da ma'aikatan gwamnatin Kano, a kan dabarun aiki

Kwalejin hukumar gudanarwar ma'aikata ta ƙasa, ASCON, na gudanar da taron horas wa na makwanni biyu, ga rukunin ma'aikatan jihar Kano, da ke matakin albashi na 13 zuwa 14.
Taron horaswar karo na 25, na gudana ne haɗin gwiwa da gwamnatin Kano, a ɗakin taro na Ɗakin Karatu na jihar Kano (State Library) an shirya shi ne domin a ƙara wa ma'aikatan ilimi a kan dabarun ƙwarewar aiki, da sanin yadda ake aiwatar da ayyukan gwamnati (Administration).
Da take jawabi a madadin Darakta Janar na ASCON, Mataimakiyar A.O Olabimitan, Mataimakiyar Daraktar sashen horaswa ta hukumar ASCON, ta ce an shirya taron ne domin horas da ma'aikatan ta yadda za su samu ƙarin ƙwarewa a fagen aiki.
A yayin da yake jawabi Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir, da ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin jihar Alhaji Umar Farouk, a yayin taron, ya jaddada cewa gwamnatin sa za ta cigaba da tallafa wa shirye-shiryen horas da ma'aikata domin inganta ƙwarewar su, da ƙarfafa aikin gwamnati.
Ya kuma ce gwamnatin Kano, ba za ta gajiya ba wajen ƙarfafa cibiyoyin gwamnati da samar da ma'aikatan da za su taka rawar gani wajen ci gaban tattalin arziƙi da zamanantar da jihar ta Kano.
Itama a nata ɓangaren, Shugabar Ma'aikatan Gwamnatin jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Mai-Mota, ta ce an shirya taron horas da ma'aikatan ne domin gina ƙwararrun ma'aikata masu nagarta, gaskiya da riƙon amana.
Da yake bayyana jin daɗin su, guda daga cikin mahalarta taron horaswar, Musa Ibrahim Ahmad (Best Seller) ya miƙa godiyar sa ga ASCON, bisa yadda suka zaɓo gogaggun masana inda suke shayar da su ilimi.
Ya kuma miƙa godiyar su ga Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa dawo musu da wannan muhimmiyar dama ta samun horaswar, wadda gwamnatocin baya suka yi watsi da ita.
Tashar Dala FM Kano ta ruwaito cewa, an fara baiwa ma'aikatan horon ne a ranar Litinin 22 ga Yuni, inda za a kammala zuwa 3 ga Yuli, 2026.



