Koma Labarai
Labarai

Gwamnatin Kano ta fara rangadin duba matsalolin da matatun ruwan yankunan karkara ke fuskanta don gyara, da saɓunta su.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Gwamnatin Kano ta fara rangadin duba matsalolin da matatun ruwan yankunan karkara ke fuskanta don gyara, da saɓunta su.

Gwamnatin jihar Kano ta fara wani ran gadi na ziyartar matatun da ke samar da ruwa a yankunan karkara, domin duba matsalolin da matatun su ke fuskanta tare da tsara matakan gyara da saɓunta su.

Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Ma'aikatar albarkatun ruwa, da Muhalli da Sauyin yanayi, Dr. Ɗahir Muhammad Hashim, ya fitar ga manema labarai a ranar Alhamis 19 ga Yuni, 2026.

Dr. Ɗahir Hashim, ya ce yayin rangadin Ma'aikatar ta yi haɗin gwiwa da Kwamishinan Ma'aikatar Ƙananan Hukumomi da masarautu, Kwamishinan Ma'aikatar wutar lantarki da tsaftace makamashi, Kwamishinan Ma'aikatar raya karkara da ci gaban al'umma.

Ya kuma ce a yayin rangadin, sun ziyarci matatar ruwan Kusalla wadda ke samar da ruwa ga ƙananan hukumomin Karaye, Kiru da Gwarzo, da matatar ruwan Pada mai samar da ruwa ga Gwarzo, da matatar ruwan Magaga wadda ke samar da ruwa ga Gwarzo da Kabo, sai kuma matatar ruwan Guzuguzu mai samar da ruwa ga ƙananan hukumomin Kabo da Rimin Gado.

"Mun tantance matsalolin da kowace matata ke fuskanta tare da tsara matakan gyara da saɓunta su domin aiwatarwa bisa sahalewar Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, in ji Kwamishinan.”

Haka kuma, Dr. Ɗahir, ya tabbatar wa al'ummar Jihar Kano, musamman mazauna ƙananan hukumomin Karaye, Kiru, Gwarzo, Kabo da Rimin Gado, cewa, gwamnatin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta himmatu wajen dawo da cikakken aiki ga waɗannan matatun ruwa, wajen gyara su tare da tabbatar da wadataccen ruwan sha ga al'ummomin da abin ya shafa.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya ruwaito cewa, a kwanakin baya ne dai Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da shirin farfaɗo da manyan matatun ruwa, da masu samar da ruwa a cikin birnin Kano, sakamakon yadda ake fuskantar ƙarancin ruwan.

Ready to PlayDala FM88.5 FM