Koma Labarai
Masarauta

Masu riƙe da masarautun gargajiya ku dasa Bishiyoyi don rage ƙwararar hamada a yankunan ku - Sarkin Kano

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Masu riƙe da masarautun gargajiya ku dasa Bishiyoyi don rage ƙwararar hamada a yankunan ku - Sarkin Kano

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya yi kira ga Hakimai, da dagatai da kuma masu unguwanni a jihar nan, da su mayar da hankali wajen dasa bishiyoyi a yankunansu domin rage kwararowar hamada.‎

‎Sarkin ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da dashen bishiyoyi a fadar Sarkin da ke Kofar Kudu, tare da Kwamishinan ruwa da Muhalli da sauyin yanayi na jihar Kano Dakta Dahiru Muhammad Hashim, suka kai masa ziyara yau a fadarsa.

‎khalifa Muhammadu Sanusi na biyu ya kuma ce dasa bishiya tana da matukar muhimmanci a rayuwar al'umma ta hanyar bada iska, da kuma samar da yanayi mai kyau a cikin al'umma baki ɗaya.

‎A nasa jawabin Kwamishinan ruwa da muhalli da sauyin yanayi na Kano, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya kuma ce sun je fadar ne domin sanar da sarki irin aikin da hukumar muhalli take yi na ganin an dasa bishiyoyin a kananan hukumomin jihar 44, domin magance matsalolin kwaraowar hamada.

‎Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, kwamishinan ya ƙara da cewa za su dasa bishiyoyin sama da miliyan goma a fadin jihar Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM