Koma Labarai
Labarai

Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta ƙara samar da kuɗaɗe ga manyan makarantu a jihar don bunƙasa ilimin ɗalibai

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Majalisa ta buƙaci gwamnatin Kano ta ƙara samar da kuɗaɗe ga manyan makarantu a jihar don bunƙasa ilimin ɗalibai

Majalisar dokokin Kano ta buƙaci Gwamnatin jihar da ta ƙara ƙaimi wajen samar da kuɗaɗe ga manyan makarantun jihar domin ƙara bunƙasa ilimin ɗalibai a faɗin jihar.

Shugaban kwamitin manyan makarantu, kuma shugaban masu rinjaye na majalisar Lawan Hussaini Dala ne ya buƙaci hakan, yayin wata ziyara da kwamitin ya kai makarantar Legal a ranar Litinin 13 ga Yuli, 2026.

Hon. Lawan Hussaini ya ƙara da cewa, ta hanyar ƙara kuɗaɗen ga manyan makarantun ne kaɗai za a iya samar da hanyoyin taimakawa ɗaliban jihar wajen bunƙasa ilimin su.

Babban sakatare a ma'aikatar kula da manyan makarantu a jihar Kano, Dakta Salahuddin Habibu, ya bayyana ziyarar da cewa abu ne mai kyau da zai taimaka wa ɗaliban a karatun su.

Kazalika, yayin ziyarar mukaddashin shugaban kwalejin ilimi ta Malam Aminu Kano, Dakta Ali Tamasi Mu'az, ya yabawa kokarin da majalissar dokoki ta Kano takeyi wajen cigaban ilimin ɗalibai a faɗin jihar.

Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Sunusi Shu'aibu Musa ya ruwaito cewa, daga cikin ƴan tawagar kwamitin akwai shugaban kwamitin Ali Lawan Alhassan kuma Dan majalissar dokoki mai wakiltar ƙaramar hukumar Wudil.

Ready to PlayDala FM88.5 FM