Majalisa ta yi karatu na biyu a dokar samar da hukumar da za ta kula da yadda ake cajar al'umma Haraji barkatai a Kano.

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi karatu na biyu a ƙudirin samar da hukumar Tsare-tsare da cigaban Kano, ta Kano State Development Planning and Development Council, da za ta kula da yadda ake cajar al'umma Haraji barkatai idan aka kafa ta.
Da yake karanto dokar a zaman majalisar na yau, shugaban masu rinjaye Lawan Husaini Dala, ya ce hukumar za ta yi aiki ne da ƙananan hukumomin jihar 44, wanda dokar za ta hana kwararowar shigowar al'ummar karkara cikin gari.
Haka zalika, a zaman majalisar na yau Talata, ta majalisar yi wa dokar kafa kwalejin Yusuf Maitama Sule da ke Ghari karatu na biyu, wanda idan an kafa ta za ta rinƙa bayar da shaidar karatu ta NCE.
Wakilinmu na majalisar dokokin jihar Kano Sunusi Shuaib Musa, ya ruwaito cewa, majalisar ta karɓi ƙudirin gyaran hanya da ta tashi daga Kundu zuwa Ɗangarko a ƙaramar hukumar Rano.



