Koma Labarai
Tsaro

Tinubu ya umarci shugabannin tsaro su gaggauta tarwatsa sansanin ’yan ta’adda a Najeriya.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Tinubu ya umarci shugabannin tsaro su gaggauta tarwatsa sansanin ’yan ta’adda a Najeriya.

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umarci shugabannin hukumomin tsaro da su gaggauta ceto dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su a faɗin ƙasar.

Shugaban ya kuma buƙacin shugabannin tsaron da su tabbatar da cewa babu wani sansanin ’yan ta’adda ko na ’yan bindiga da ya rage a ko’ina a Najeriya.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis 15 ga watan Octoba, 2026, yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja, jim kaɗan bayan kammala wani babban taron tsaro na musamman da Shugaba Tinubu ya jagoranta.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM