Koma Labarai
Shari'a

Kotu ta tsare matar da ake zargi da safarar makamai zuwa ga ƴan bindiga a Kaduna

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Kotu ta tsare matar da ake zargi da safarar makamai zuwa ga ƴan bindiga a Kaduna

Babbar Kotun jiha mai zamanta a Dogarawa ta jihar Kaduna, ta aike da wata mata gidan gyaran hali bisa zargin ta da laifin safarar makamai zuwa ga ƴan bindiga.

Matar mai suna Bilkisu Hamza ana zargin ta ne da laifin samu da harsasan bindiga guda 138.

Ƙunshin tuhumar ya bayyana cewar hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ce ta kama matar a lokacin da ta shiga wani daji a yankin Kafancan ta karɓo waɗannan miyagun kaya.

A zaman kotun na ranar Alhamis 9 ga Yuli, 2026, an karanta wa matar ƙunshin zarge-zargen da ake yi mata sai dai ta musanta.

Wakilin Dala FM Kano, Yusuf Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, kotun ta yi umurni da a tsare ta a gidan ajiya da gyaran hali har zuwa ranar 9 ga Agusta, 2026.

Ready to PlayDala FM88.5 FM