Hukumar kula da Shari'a ta buƙaci Alƙalin kotun Bebeji da ya yi ritayar dole bayan cin kuɗin ƴan Sha'ri'a a Kano.

Hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta Jihar Kano, ta umarci Alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci ta Babeji, Alkali Aliyu Yahaya Muhammad, da ya yi ritayar dole ba tare da ɓata lokaci ba.
Wannan na cikin sanarwar Mai magana da yawun babbar Kotun Kano, Baba Jibo Ibrahim, ya aiko wa Dala FM Kano, a ranar Litinin 6 ga Yuli, 2026.
Ya ce ɗaukar wannan mataki ya biyo bayan kwamitin korafe-korafen al’umma na bangaren shari’a ya kafa hujja da zargin karbar cin hanci da rashawa da ake yi masa a kan wata ƙara mai lamba CV/474/2024, a tsakanin Talatu Ibrahim da Muntari Abubakar Baguda.
Hukumar ta kuma umarce shi da ya mayar da kudaden da ya karɓa a matsayin rashawa har naira 250,000.00.
Sanarwar ta ce Hukumar ta kuma amince da dakatarwa ba tare da biyan albashi ba na tsawon watanni hudu (4) ga Magatakardan kotun shari’ar muslunci ta Babeji, Ibrahim Ahmad Ibrahim, bayan da ya amince da karɓar wani ɓangare na kuɗaɗen da aka karɓa a matsayin cin hanci a shari’ar da aka ambata a sama.
Hukumar da ke kula da harkokin shari’a ta Jihar Kano, ta bayyana ɗaukar wannan mataki ne a taron ta na 90 da ta gudanar a ranar 3 ga watan Yuli, 2026.
Taron ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin Babbar Jojin Kano Justice Dije Abdu Aboki, bisa la’akari da rahotanni da shawarwarin kwamitin karfar ƙorafe-ƙorafen jama’a na shari’a kan koke-koke da ladabtarwa da suka shafi alkalai da ma’aikatan kotunan jihar Kano.
Sanarwar ta kuma ce, bayan tattaunawa na tsanaki, hukumar ta amince da daukar matakan ladabtarwa da suka dace da kundin tsarin mulkin kasar na tabbatar da gaskiya da rikon amana, da kuma amincewar jama'a kan gudanar da shari'a.



