Gwamnatin Kano ta ƙudiri aniyar sanya ƙafar wando ɗaya da masu fatauci da shan miyagun ƙwayoyi a fadin jihar
Hassan Mamuda Ya'u 0 views

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabiru Yusuf, ya ƙaddamar da kwamitin yaƙi da miyagun ƙwayoyi, a fadar gwamnatin jihar, ranar Laraba 22 ga Yuli, 2026.
Yayin da yake ƙaddamar da kwamitin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matukar takaicin sa bisa yadda shaye-shayen ƙwayoyi ke cigaba da haddasa faɗace-faɗacen daba da kwacen Waya, da sauran miyagun dabi’u.
WAkilinmu Nasir Salisu Zango ya ruwaito cewa, Gwamna Yusif ya ce gwamnatin Kano ta ƙudiri aniyar sanya ƙafar wando ɗaya da masu fatauci da shan miyagun ƙwayoyi a fadin jihar Kano.



