Koma Labarai
Labarai

Na janye shirina na buɗe "Film House" a unguwar Ɗorayi - Abdulrrazak Sultan

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Na janye shirina na buɗe "Film House" a unguwar Ɗorayi - Abdulrrazak Sultan

Mamallakin ginin "Film House" da ke Ɗorayi unguwar Bello, Alhaji Abdurrazak Sultan, ya sanar da janye shirinsa na bude wa gaba ɗaya, biyo bayan korafe-korafe da al'ummar yankin suka yi.

Abdurrazak Sultan ya bayyana hakan ne yayin wata ganawarsa da manema labarai, inda ya ce ya ɗauki matakin ne domin mutunta ra'ayin al'umma da kuma tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin mazauna yankin.

Sultan ya kuma ce tun bayan da aka fara bayyana shirin gina Film House ɗin, al'ummar Ɗorayi da wasu masu ruwa da tsaki suka nuna damuwa, inda suka nemi a sake nazari kan amfani da wurin ta yadda zai fi amfani ga ci gaban matasa da ma al'umma baki ɗaya.

Ready to PlayDala FM88.5 FM