Koma Labarai
Tsaro

Ya kamata gwamnatin Kano ta kafa hukumar da za ta kula da harkokin dillanci don kawo tsafta a ciki - Ƙungiyar KPADA

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Ya kamata gwamnatin Kano ta kafa hukumar da za ta kula da harkokin dillanci don kawo tsafta a ciki - Ƙungiyar KPADA

Ƙungiyar masu sayar da filaye da gidaje da bada haya ta jihar Kano, (KPADA) ta ce akwai buƙatar gwamnatin jihar ta samar da hukuma tare da samar da dokoki, wadda za ta rinƙa kula da harkokin dillanci domin ƙara tsaftace harkar tare da magance matsalar tsaro.

Shugaban Ƙungiyar ta Kpada a Kano, Alhaji Isah Jibril Isah (Kaci-ƙasa) ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Dala FM Kano, biyo bayan ziyarar da suka kai ofishin shugaban hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci ta jihar Kano, (Anti Curroption), Kwamared Sa'idu Yahaya, a ranar Alhamis 2 ga Yuli, 2026.

Ya ce sun kai ziyarar ne bisa yadda ake yawan samun ƙorafe-ƙorafe a kan wasu ɓata garin da suke shigowa harkar dillanci suna cutar mutane, a don haka ne suka ƙulla alaƙar aiki da shi domin ganin gwamnati ta shigo cikin harkar don kawo sauyi.

Isah Jibril Isah Kaci-ƙasa ya kuma yi kira ga gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya ƙara shigowa cikin harkokin masu sayar da filaye da gidaje da kuma bada haya, domin ganin an magance ƙalubalen da ake fuskanta a ciki.

A cewar sa, "Yanzu harkar dillancin ta tumbatsa domin cikin masu yi akwai wasu ɓata gari da ake kira da Ƴan Ƙasa ta Allah ce, da Dillali Shaho, da kuma dillalan tsaye, da sauran su, waɗanda ke cutar mutane a harkar dillanci, waɗanda muke yaƙi da su," in ji Kaci-ƙasa.

Ya kuma ce idan har Majalisar dokokin Kano, ta yi doka mai tsauri a kan harkar dillanci a jihar, babu makawa za a samu canji ta ɓangarorin daban-daban, ciki har da daƙile cutar mutane, da yaƙi da matsalar tsaro.

Ya kuma ce ƙungiyar su ta KPADA, za ta yi duk mai yiyuwa wajen baiwa hukumomin tsaro da na gwamnati haɗin haɗin kan da ya dace domin ganin an ƙara kawo tsafta a cikin sana'ar sayar da filaye da gidaje da kuma bada haya a Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM