Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya soki yadda ake tafiyar da shari’ar El-Rufa'i a kotu

Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya bayyana damuwarsa kan yadda ake gudanar da shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, yana mai cewa dole ne a tabbatar da adalci da bin ƙa’ida ba tare da nuna bambanci ba.
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake gabatar da Maƙala a babban taron masu ruwa da tsaki na ƙasa, inda ya yi nuni da cewa akwai buƙatar a mutunta haƙƙin duk wanda ake tuhuma, ciki har da damar samun beli kamar yadda doka ta tanada, yana mai cewa hakan na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da gaskiya a tsarin shari’a.
Ya kuma bayyana El-Rufai a matsayin misali da ya nuna cewa dole ne a riƙa tafiyar da shari’o’i cikin gaskiya, nesa da duk wani abin da zai iya nuna son rai ko tauye haƙƙin ɗan Adam.
A cewarsa, tsarin shari’a mai ƙarfi shi ne wanda ke kare haƙƙin kowa tare da tabbatar da cewa ana bin doka yadda ya kamata ba tare da wariya ba.



