Koma Labarai
Labarai

INEC ta musanta zargin cewa ana iya kashe na’urar BVAS ta hanyar nesa kafin a kammala zaɓe.

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
INEC ta musanta zargin cewa ana iya kashe na’urar BVAS ta hanyar nesa kafin a kammala zaɓe.

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta musanta iƙirarin cewa ana iya kashe na’urar tantance masu zaɓe ta BVAS ta hanyar nesa kafin a kammala zaɓe.

Hukumar ta bayyana cewa wannan batu ba gaskiya ba ne, kuma yana yaudarar al’umma.

INEC ta bayyana hakan ne a cikin wani saƙo da ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata 17 ga watan Nuwamba, 2026.

Hukumar ta kuma yi watsi da zargin cewa ana iya rasa bayanan sakamakon zaɓe ta hanyar amfani da irin wannan hanya.

Kafar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, INEC ta ce ta yi wannan bayani ne domin wayar da kan jama’a da kuma fayyace yadda na’urar BVAS ke aiki.

Ready to PlayDala FM • 88.5 FM