Kwankwasiyya ta zargi gwamnatin Kano da yunƙurin ciyo bashin Naira biliyan 55 ga kananan hukumomi.

Kungiyar Kwankwasiyya ta bukaci Gwamnatin Kano ta yi karin bayani kan rahotannin shirin karbo rancen kusan Naira biliyan 55 daga bankin kasuwanci, wanda za a dora wa kananan hukumomi 44 na Kano.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Dr Habibu Sale Mohammed, ya sanya wa hannu a ranar Lahadi 18 ga watan Oktoba, 2026.
Ƙungiyar ta ce ana sa ran kowace karamar hukuma za ta dauki nauyin biyan kusan Naira biliyan 1.3, a rancen idan an yi.
Ta ce ana zargin za a yi amfani da kudin wajen gina cibiyoyin jarrabawar kwamfuta (CBT), da wani aikin da ba a bayyana sunansa ba, da kuma shirin tallafa wa jama’a.
Kungiyar ta kuma buƙaci gwamnati ta bayyana cikakken bayani kan ayyukan, inda za a gudanar da su, waɗanda za su ci gajiyar shirin da kuma yadda za a biya bashin.
Kazalika, ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan lokacin da aka gabatar da shirin, duba da kusantowar zaben 2027, tana mai cewa ya kamata a samar da matakan tabbatar da cewa ba a karkatar da kuɗin zuwa harkokin siyasa ba.
Sai dai kungiyar ta jaddada cewa ba ta zargi gwamnati da shirin amfani da bashin wajen yakin neman zaɓe ba.
Haka kuma, Kwankwasiyya ta buƙaci gwamnatin Kano da ta yi bayani kan kuɗaɗen da ƙananan hukumomin suka bayar a wani shirin tallafa wa mata a baya, ciki har da jimillar kuɗin da aka tara, waɗanda suka amfana da su da kuma dalilin da ya sa shirin ya tsaya bayan ƙasa da watanni 10, kamar yadda ta yi zargi.
Ta kuma yi kira ga Majalisar Dokokin Jihar Kano da ta bayyana ko ta amince da shirin rancen, tare da wallafa takardun amincewar idan hakan ya faru.
Kungiyar ta bukaci bankin da ake zargin zai bayar da rancen da ya tabbatar da halaccin yarjejeniyar, ikon kananan hukumomin karɓo bashi da kuma karfin su na biyan kuɗin.



