Koma Labarai
Labarai

Hukumar jin daɗin Alhazan Kano ta dawo da sama da Kaya 130 da Alhazai suka bari a Saudiyya

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Hukumar jin daɗin Alhazan Kano ta dawo da sama da Kaya 130 da Alhazai suka bari a Saudiyya

Hukumar Jin daɗin Alhazai ta Jihar Kano, ta bayyana cewa ta dawo da fiye da kaya 130 na alhazan jihar da aka bari a masaukansu, da kuma filayen jiragen sama na ƙasar Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.

Darakta Janar na Hukumar Alhaji Abubakar Ibrahim Matawalle, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a ranar Talata 7 ga Yuli, 2026, domin bayyana manyan nasarorin da aka samu a aikin Hajjin bana.

Ya ce hukumar ta dawo da kusan kaya 30 da alhazai suka bari a masaukansu, sannan ta sake dawo da fiye da kaya 100, waɗanda suka haɗa da manyan akwatuna da jakunkunan hannu da aka bari a filayen jiragen sama na Saudiyya.

A cewarsa, "Hukumar mu ta ɗauki hayar wani kamfanin jigilar kaya na ƙasa da ƙasa, domin dawo da dukkan kayayyakin zuwa Kano, inda za a miƙa su ga masu su," in ji shi.

Alhaji Abubakar Matawalle ya ce wannan nasara ta nuna ƙudirin hukumar na kare dukiyoyin alhazan Kano, yana mai cewa babu ko da Alhaji ɗaya daga jihar da aka bari a Saudiyya bayan kammala aikin Hajjin shekarar 2026.

Ready to PlayDala FM88.5 FM