Koma Labarai
Masarauta

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya naɗa Abba Ibrahim a matsayin dagacin Kududdufawa

Hassan Mamuda Ya'u 0 views
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya naɗa Abba Ibrahim a matsayin dagacin Kududdufawa

‎Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya naɗa Mallam Abba Ibrahim, a matsayin sabon dagacin garin Kududdufawa da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a jihar.

Sarkin ya naɗa sabon dagacin ne a fadar masarautar da ke Ƙofar Kudu a Kano, ranar Laraba 24 ga Yuni, 2026.

‎Bayan kammala naɗin nasa ne mai martaba Sarki Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya horeshi da ya zauna lafiya da al'ummarsa, ya kuma  sanya idanu kan harkokin tsaro, lafiya da ilimi a garin na Kududdufawa.

‎A nasa jawabin sabon dagacin garin Kududdufawa Malam Abba Ibrahim, ya bayyana farin cikinsa bisa naɗa shi da mai maraba sarkin na Kano ya yi a matsayin dagacin garin Kududdufawa.

Mallam Abba ya kuma ce zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da rikon amana, tare da kira ga al'ummar garin nasa da su bashi haɗin kai da goyon baya a kowane lokaci.

‎Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da'u Abdullahi ya rawaito cewa, al'ummar garin na Kududdufawa da dama ne suka halarci taron naɗin dagacin a fadar masarautar Kano.

Ready to PlayDala FM88.5 FM